peperonity.net
Welcome, guest. You are not logged in.
Log in or join for free!
 
Stay logged in
Forgot login details?

Login
Stay logged in

For free!
Get started!

Mobile Blog


dadylasting.peperonity.net

Sarkakiyar soyayya labarin soyayya

03.11.2014 15:14 EST
SARKAKIYAR SOYAYYA
.
Admin dadylasting me zamani

sararin samaniya dauke yake da gajimare hakan ne yasanya garin yayi sanyi me dadi gami da iska me busowa a hankali.
Garin cike yake da jama'a ko ina duk inda ka waiga ba abinda zaka gani illah kawunan mutuna da muryoyinsu
ba komai bane ya haddasa haka illah ana gobe sallah burin kowa yaje kasuwa yayi siyayyan sallah.¤
***** *******
******
tashi wata daga garejin gyaran mota kenan
bayan na wanke jikina nasa kayan gida harna nufi wajen mashin dina sainaji ana kirana dady dady cikin sauri na juyo domin cewa muryan ogana naji....
Gani oga abinda nace kenan lokacin dana karasa wajensa. Yaje dani dady ga key din motata kaje kashawo min mai kadawo
nace to amma ba'ason raina ba saboda akwai wani wasa da'akeyi yau a kano clup inaso naje.
.............................
Cikin sauri naje inda ogan mu yake aje motan sa na tuka na fito dashi waje ina fitowa sainaji ana D...LASTING ina juyawa sainaga yarinyar datake kawo mana abincine dama naci abinci ban biyata ba. Kawai na daga mata hannu alamun ina zuwa.
...............................
A hankali nake tuka motan ba wani gudun kirki nakeyi ba saboda garin akwai cinkoso dayawa.
Tafiya nake a hankali nakunna wakan nura m inuwa [abin sona]
tun daga nesa idanuwata suka hangomin wata kyakkyawar budurwa ajin farko acikin yan mata. Kyawun nata yawuci hankalin me kwantace.
Ina matsowa kusa sainaga cewa ta tsaya agefen titi ajikin wata mota da alama cewa motan nata ya bacine.
Harna wuceta sainayi ribas na dawo nayi fakin din motata a gefe.
Ina zuwa wajen tashin farko nace da ita
AMINCIN ALLAH YA TABBATA GA YAN MATA KYAWAWA KAMAN YANDA KIKE KYAKKYAWA.
Fuska tayi ko daga ido batayi ta kalle niba balle tasan da'akwai mutum a wajen.
Nakara da cewa.
Nasan cewa dama zaiyi wuya ki amsa slm ta saboda ba kimarki bane a matsayinki na babbar mace me aji da kima ki tsaya kina kula na miji akan titi?? Nikaina nasan nayi kuskure amma kisani cewa bakomai bane yasa natsaya illa naga alaman kaman kina bukatan taimako. Amma saide wani bari na zuciyata ya gayamin cewa ba lalle bane ki amince da taimakon dazan maki inda inada yakinin cewa ke daban kike a cikin yan mata.
Ina zuwa daidainan a maganata sainayi shiru.
Saida takai kusan 30 secon kafin nan ta juyo ta watsamin wani kallo wanda yasa naji jikina ya mutu.
Ta budi bakinta tace taya akayi kasan ina bukatan taimako??
Tsabagen tsananin zakin muryata saida yasa na manta a inda nake. Ta kara watsomin tambayan a karo na 2. kafin na budi maki dakar nace da ita. Naga kaman motanki ta samu matsala kina bukatan makaniki tace eh. Nace idan zaki amince yanzu na kira maki maka nikena yazo ya gyara maki tace to a hankali.
Nace bari na dauko wayata acikin mota ina shiga cikin mota na dauko wayata na bugawa abokina waya me suna salisu shima makanike ne Yana gyaran motane akan titin ringi road. Kuma abokinane sosai. Kawai saina gayamai wasu magana.
Fitowa nayi nasameta nace na kira maki makanikin yana zuwa
ba'afi minti goma 15 ba saiga salisu yazo
yana zuwa nace mai wannan motan zaka duba mana taki tashi yace to.
****
cikin yan mintina harya gama gyaran motan. Yatashi motan. Ta budi baki tace nawa za'a biyaka yace ai oga yabiya tace waye oga ya nunani. Hmm tamin murmushi me taushi tace nagode. Nace bakomai
sainace dan allah wani taimako nake nema tace tame. Nace kozan iya samun phone no. Naki da address kawai saitayi murmushi ta mikomin wani kati na'amsa nace amma saide bansan sunan gimbiyan ba?? Tace sunana AMEERA nace nice name nikuma sunana sa'id amma zaki'iya kirana da [dadylasting]
.........................
Ade haka muka rabu da'ita amma da alama ina ganin nasamu shiga.
***********
washe gari da sassafe dayake ranan sallah ne bayan mundawo daga idi. Kawai saina bugawa ameera waya mundade muna hira daga karshe nake tambayanta yaushe zanzo gidansu. Tace duk randa kashirya. Nace zanzo da yamma.
..............
Da misalin karfe 4pm nashirya nayi niyar tafiya gidansu amira.
Saide amsamu matsala naje wajen yayana yaban motansa nafita dashi shima yace fita zaiyi.
Kawai saina karasa gidanmu nayi sa'an babana yana gida cikin sauri na garzaya cikin dakinsa na dauko mukullin motansa ba tare dana tambaye saba.
**********
gudu nakeyi sosai acikin motan na nufi hanyar gidansu ameera dake nasarawa G.R.A gida me number xxxx bansha wuya ba wajen gane gidansu
saina tsaya akofan gidansu nayi mata waya nace ganinan a kofan gidansu tace inshigo horn kawai nayi me gadi ya budemin gat nashiga naje na'aje motata a inda ake aje motoci dannaga motoci dayawa awajen
fitowata daga motan keda wuya idanuwana sukamin arba da wasu manyan abubuwa wanda yasa nayi dana sanin shigowata gidansu
amma ina ai tuni an...........

.....................................
Hankalina yayi balakin tashi sakamakon abinda idanuwana suka ganemin acikin gidan
bakomai nagani ba illa wasu manyan karnika wanda nasan cewa koya nayi motsi zasu iya cinye ne domin cewa guda 1 daga cikinsu yakai girman zaki.
Nan take jikina yafara tsuma..
Ahankali nabi na fada cikin motata kafinnan na buga mata waya nace na shigo cikin gidanku amma naga karnika kizo mutafi tare ciki tace to.
Ba'afi binti 3 dayin wayan ba na hangota tayi wani shegen shiga tun kafin takaraso inda nake tuni nazama kankara.
Tazo sai magana takemin amma banjima saboda nayi nisa acikin wata sabuwar duniya saida ta dafa kafada ta kafin nayi dogon numfashi nadawo cikin hayyacina. Tace dani lafiya D...LASTING tunanin me kakeyi. Nace da'ita babu komai. Ahaka muka karasa da ita cikin gidansu zuwa falon saukan baki shigana cikin falon keda wuya nafara kauyanci saboda ma alokacin dana taka kafet din falon saida nayi kara na dauka zan nutse kasane. Ashe laushin kafet dinne.
Tace dani lafiya kayi kara nace nadan fame targadena ne. Tace sannu. Nace yauwa
............................
mundade muna hira da'ita kafin mukayi sallama muka rabu amma ba'ason ranta ba.
******
nadawo gida cikin farin ciki da annashuwa kasancewar nasamu shiga sosai wajen gimbiya ameera. Ada nayi tunanin cewa zansha wuya kafin ta amince da soyayya ta.
Saikuma gashi bansha wuya ba.
........................
Ina shigowa harabar cikin gidan mu nayi fakin din mota. Na wuce direct dakina domin na huta.
Ina shiga dakina naji handset dina yayi kara alamun an turo wasika cikin sauri na bude wasikan sainaga anyi rubutu kaman haka.
ASSALAMA ALAIKUM YAKAI SAHIBINA RABIN RAINA MIJINA NA GOBE SONKA YAYI GIRMA ACIKIN ZUCIYATA WANDA BANSAN IYA KACINSA BA DA'ACE ZAKA ZAMA S NIKUMA NAZAMA O DA MUNHADA WATA KALMA ME SUNA [SO] INA SONKA KAMAN YANDA NAKE SON KAINA DAFATAN KA'ISA GIDA LAFIYA
ina kammala karanta wannan wasikan nayi murmushi. Kafin nima na mayar mata da replay kaman haka.
SARAUNIYAR ZUCIYATA.
DUK LOKACIN DANA RUFE IDO KE NAKE GANI. HAKANAN IDAN NA BUDE
YAUSHE ZAN DAINA SONKI KUWA ACIKIN ZUCIYATA?
BABU MAI IYA CE GA RANAR. DON HAKA KENAN SONKI YANA ZUCIYATA HAR ABADA.
DA'ACE ZAKI ZAMA FUKAFUKIN DAMA NIKUMA NA ZAMA NA HAGU DOMIN MUTARU MUTADA TSUNTSUN SOYAYYA.
Ina zuwa daidainan a wasikata saina tura mata.
*************
ahaka muka kasance da ameera muna soyayya me zafi cikin kwanciyar hankali da kaunar juna.
Saide kash ta waje daya na kwafsa nayi mata karya dayawa.
Kuma tunda nake bantaba zuwa da mota kala 1 sau 2 wajenta ba. Kuma bana zuwa da motan kasa da miliyan 3 sai sama da haka kasancewar yayana mota yake siyarwa nikuma makanike ne.
...................
Wata ranan juma'a da misalin karfe 5pm na shirya na dauki mota kirar [bmw x5] awannan lokacin kalan motan duka basufi guda 5 ba a 9ja.
Naje wajen ameera dashi mundade muna hira daga karshe nake gaya mata insha allahu zanje abuja gobe amma ranan lahadi zandawo tace allah yakiyaye hanya dan allah banda kalle kallen yan mata kawai sainayi dariya nace.
Ke kina tunani cewa harda'akwai wata ya mace dazan kalla fadin duniya bayan inada sarauniyar yan mata.
Tayi murmushi me taushi agareni wanda aduk lokacin datayi murmushin hankalina kwanciya yakeyi gami da kara sonta acikin zuciyata. [ashe karya nake mata akan zanje abuja]
************
ina gareji da misalin karfe 2pm bayan na idar da sallah azahar naji wayata tayi ringi ina dauka naga ai ameera ce. mundan taba hira kadan harnake gaya mata ayanzu haka na sauka a garin abuja lafiya.
Tace hmm nagodewa allah. Sai mukayi slm
..................
Banfi minti ashirin ba da kammala wayan naji ogana yana kirana dady dady dady nace na'am oga yace kadakata da aikin da kakeyi kaje gacan wata mota brama kayi mata service nace to.
Ina zuwa na kunce bakin man motan da filta da kuma nosin. Naje wajen ogana nace oga kaban kudi nace nasiyi bakin mai da filta da injector cliner domin awanke nosin yacemin kaje kasan bishiya akai yan mata awajen ka karbi kudin nace to.
Ina zuwa batare dana hankara ba nace hajiba kiban kudi nasayo kayan gyara
budurwar tana juyowa sainaga ai ameera ce. Tana kallona ta dafe kirji tace D...Lasting nanne abujan? Dama kai mayaudari ne.
A haba ina kawai saina ruga da gudu nayi wajen gareji.
INA ASHE GUDUN BANZA NAYI HAR GIDA ZATA BIYONI
TAMIN.....

..................................
Cikin sauri na juya da gudu nabar cikin garejin ko kayana ban chanja ba. Ina fita ko mashin dina ban dauka ba gudun karna tsaya dauka tazo tasa meni.
Ina fita bakin titin hadejia road dayake garejin namu a hadejia road yake kusa da shop she---she. Cikin sauri na tari me adaidaita sahu nace yakaini tarauni.
Ana saukeni a tarauni na rasa inde zanje kawai sainayi shawaran inkoma gida na bugawa wani dan garejin mu waya nace yatawo min da mashin dina gida yace to. Haryake gayamin cewa ameera tasha kuka acikin garejin waina yaudareta.
Sauri nayi na kashe wayan na fada cikin wani botiq nasayi kaya domin cewa yanda akemin kallon babban yaro a unguwar mu bazan iya shiga da kayan gareji ba.
Bayan nasiyi kaya na chanja saina bugawa abokin harkata usman na gayamai cewa yaufa rana ta kwabe. Kazo da motarka ka daukeni inanan kasuwar tarauni kasan bazan iya hawa adaidaita sahu inzo gidaba dan kasan ana biki akan layinmu akwai yan mata dayawa yace to.
Minti 20 yayi yawa saiga usman yazo acikin motansa joka ya daukeni yakawo ni gida. Nake gayamai idan nasamu nutsuwa zan basa labarin abinda ya faru dani yake ok.
************
ina shiga cikin gida ...


This page:
Help/FAQ | Terms | Imprint
Home People Pictures Videos Sites Blogs Chat
Top
.