peperonity.net
Welcome, guest. You are not logged in.
Log in or join for free!
 
Stay logged in
Forgot login details?

Login
Stay logged in

For free!
Get started!

Mobile Blog


dadylasting.peperonity.net

Nayi gamo da aljana. Sabon labari

03.11.2014 15:35 EST
NAYI GAMO
admin dadylasting

rayuwar duniya kenan. Hawaye ne yake zuba acikin idanuwana babu kwakkwatawa zubowa yake saikace ankunna kan fanfo gaba daya jikina yajike da hawaye nayi kukan harna gadi sakamakon yanayin dana jefa rayuwata aciki wanda nasan cewa fitata acikin wannan yanayi abune me wuyan gaske. Nasha fadawa kangin rayuwa allah yana cire ni. Amma wannan nafada cikin babban tarko wanda fitana acikinsa bakaramin al'amari bane.
Nasan cewa mutane dayawa sunamin kallon mayen mata. Yawancima wayanda suka karanta labarai na irinsu [DANA SANI. NINA JAWA KAINA. RAYUWAR DADYLASTING DSS]
a bari guda kuma wasu sunayin kallon mutumin banza barema wa yanda suka karanta labaran nan [DADYLASTING DA FADILAT. BANZATA BA. MAFARKI NAKE. RASHIN SANI GIDAN DADI DSS]
duk irin kallon da mutane sukemin wannan be dameni ba. Illa shurin danayi kwana 2 bana kawo labarai harna farajin jita jita wai ana cewa takaremin... Ammani ko a jikina..
Duk acikin sunayena babu sunan danafi so a rayuwata kaman [ME ZAMANI]
amma a yanzu natsini sunan sakamakon abinda yafaru dani.
Ga yanda lamarin yake
******************
sararin samaniya yayi baki wuluk sakamakon hadarin daya mamaye sararin subuhana. Sai iska ake kadawa me sanyi ga yayyafi da'akeyi kadan kadan.
Dayake da daddare ne misalin karfe 11pm
nikadaine nake tafiya acikin motata tafiya nake a hankali sakamakon yayyafin da'akeyi
tafiya nake acikin motan amma gabana faduwa yake.
tun daga can nesa dani na hango wata kyakkyawar budurwa tana dagamin hannu alamun na tsaya. Ji nayi kirgina ya buga da karfi rassss sakamakon hangota danayi. Banyi niyan tsayawa ba. Amma ina zuwa daidai da ita bansan lokacin dana tsaya ba kode kafanane ya taka birki garin kidimewa ko kuma motan dakansa ya tsaya.
Tsayawa nayi kikam acikin motan nakasayin motsi
numfashina ya daukene sakamakon ganin fuskar kyakkyawar budurwa danayi
idan zan wuni inkwana ina gaya maku yanayin kyawunta bazan fadi koda rabiba. Harna farayin tunani anya mutum ce.
Tunanina ya katsene alokacin dana jiyo muryar kyakkyawar budurwar tana cewa da muryarta me dadin ji da sauraron me sauraro dan allah bawan allah ka taimaka ka ragemin hanya,
na fada a hankali nace kishiga mutafi a ina za'a ajeki tacemin bakin gada.
Tana shiga naja motan muka fara tafiya
tafiya kadan mukayi na daga idona na kalli miron mota. Abinda nagani ajikin miron shiyayi mugun tayarmin da hankali. Gani nayi kyakkyawar budurwar bayan motata tanamin gizo ta dawo tsohuwa ta dawo budurwa chanjawa takeyi zuwa siffa daban daba.
Anya ba aljana bace??
........................................
Daga idona nayi na kalli miron motan gani nayi kyakkyawar budurwa tana chanjawa ta dawo tsohuwa ta dawo budurwa. Sai chanjawa takeyi izuwa siffa siffa
bansan lokacin dana juya da sauri ba na kalli bayan motata. Ina juyawa sai muka hada ido da ita tamin wani murmushi cikin sauri na kauda kaina.
Bansan lokacin da fitsari yafito daga cikin wando naba.
XXXXXXXXXXXXXXXXXXXXXXXXXXX
cikin i'i'ina nace da ita sauka munzo bakin gada
tace to nagode bawan allah nace bakomai
tace gashi zaka tafi baka gayamin sunanka ba. Nace da'ita sunana ME'ZAMANI
nantake naga tasa dariya. Tace meyasa za kamin karya.
Nace karya kuma tace eh sbd baka gayamin sunanka ba
nace to wani suna kike so na gayamiki bayan wanda na fada maki
tace dani sunanka SA'ID
gabana faduwa yayi rass bansan lokacin dana taka motar ba natafi na barta awajen amma kuma saida nayi tafiyar sama da minti 5 inajin kuwan dariyanta acikin kunnena.
Tabbas nasan cewa nayi gamo da aljana yau.
Tafiya nake da gudu acikin motan bani da wani buri illa inganni a gida
misalin karfe 11:40 na dare na karaso cikin gidanmu ban nupi ko'ina ba. Sai cikin dakina kasancewar dare yayi nasan cewa gaba daya mutanen gidanmu sunyi barci naso na bugawa abokina waya msalihu domin nasar dashi amma sainayi tunani cewa shima yayi barci
a hankali na bude kofan dakina kasancewar gaba daya a gaje nake
kan gadona na nufa direct da nufin inkwanta nayi barci. Amma saide ina zuwa daidai bakin gadona naga wata takarda an ajeta akan gadona
""kaman daga sama naji ance dani maza ka dauki wannan takarda ka karanta abinda ke ciki"""
cikin sauri na waiga bayana amma banga kowa ba. Na kalli saman dakina shima bakomai illa fankan dayake kadawa
nantake hankalina ya kara tashi.
""nakaraji kaman daga sama a karo na 2. Maza ka dauki wannan takardan ka karanta abinda yake ciki""
bansan lokacin dana mika hannuna ba na dauki takarda na bude
XXXXXXXXXXXXX
fara karanta abinda ke cikin takardar keda wuya numfashi na ya dauki hankalina yayi balakin tashi
bansan lokacin da hawaye yafara zuba daga cikin idanuwana ba.
Wayyo duniya ina zansa kaina??
Ga abinda na karanta acikin wasikan kaman haka....
X
xx
xxx
xxxx
xxxxx
DAFATAN KANANAN LAFIYA YAKAI MASOYINA.
Kullun sonka dada karuwa yake acikin zuciyata bazan iya kirga adadin so da kaunar danake maka ba
na dade ina rubuta adadin sonka da kaunarka acikin kundin zuciyata tun tsawon wani lokaci. Amma har yanzu banga alamar zan kammala rubutun ba
wannan yana nufin sonka ba adadi.
Ina sonka sa'id kaman yanda nakeson kaina
kuma babu wata ya mace data isa ta rabani dakai
ka huta lafiya zanzo gobe muyi hira
kuma inama gargadi cewa karka sake ka gayawa kowa.
Domin inde ka gayawa wani baza kaji dadi ba
NICE MASOYIYARKA ALJANA SALEEMAT
XXXXXXXXXXXXXXXXX
haryanzu jikina fitar da gumi yake hakan ya haddasa gaba daya kayan jikina yajike saikace wanda ruwan sama yayi mai dukan tsiya
""kaman daga sama na karaji anyi magana da wata murya me dadin ji da sauraro ance haba masoyina tunanin me kake ka kwanta kayi barci mana domin cewa gobe baza ka samu barci ba zanzo mukwana muna hira""
cikin kidimewa na daga kaina na kalli sama inda nake jiyo maganan amma banga kowa ba.
Cikin karfin hali na kwanta akan gadona
amma bacci yaki zuwa
a haka na kwana cikin rashin kwanciyar hankali
XXXXXXXXXXXXXXXX
washe gari da sassafe bayan na idar da sallah asuba
natashi na shiga cikin gidan mu domin na gaidar da iyayena
bayan na gaidar da babana naje na gaidar da mahaifiyata hartake tambaya ta lafiya taga na rame kode akwai abinda yake damuna nace babu komai
cikin sauri na tashi na wuce dakina.
Da misalin karfe 10:00am bayan nayi break past naje na dauki motata da niyar in wuce office
ina zuwa jikin motata.
Ina budewa ina mata key naji ance dani kaman daga sama
""da wata katuwar murya me kama dana jaki karde kasake ka gayawa kowa abinda ke tsakanin mu. Kuma karka manta cewa duk inda kake ina tare dakai""
cikin kidimewa naja motata na fita daga cikin harabar gidan mu.
XXXXXXXXXXXX
XXXXXXXXXXXXX
da misalin karfe goma na dare na nufi dakina da niyar na kwanta amma gabana sai faduwa yake
a haka naje na kwanta amma ido na yanakan agogo karfe 11:30pm naji shiru banji alamun zuwan wani abuba.
Har bacci ya kwasheni amma ban dade acikin barci naba naji gaba 1 kasan dakina da gadona sai girgiza yakeyi dakina yayi duhu sosai. Saikuma wani kara dana keji kíiiiiiikiiiiiikiíiiiii
nan take hankalina ya tashi can sainaga dakina ya gauraye da farin haske kuma duk girgizan da dakina yakeyi ya daina
sai naji wata siririyar murya me fitar da amo me dadi ance dani sannunka da hutawa masoyi na
cikin sauri na juya bayana domin naga wacce takemin magana wata kyakkyawar budurwa na gani wanda kyawunta ya wuci hankalin me kwatance
taf dijam
.................................
Sannunka da hutawa masoyi na cikin sauri na juya domin inga wace takemin magana
wata kyakkyawar budurwa nagani a gefen gadona.
Hmm nantake na karajin bugun da zuciyata takeyi yakara karuwa
cikin tsananin tsoro da fargaba nace da'ita taya akeyi nazama masoyinki alhalin cewa ni'a iya sanina bani da wata halaka dake??
Cikin muryarta me dadi da kwantar da hankalin me sauraro. Tace dani haba dadylasting dina. Yazakace haka bayan cewa da sonka nake kwana nake tashi.
Idan baka manta ba.
Shekara biyar baya kun taba haduwa da wata mata da daddare?
Hankalina yakara tashi sbd ta tunomin da wani labari wanda banason kara tunosa a rayuwata.
Nace da'ita taya akayi kikasan wannan labarin tace dani nasan kadan daga cikin labarin shine yanzu nakeso kabani labarin cikakle
shiru nayi na kaman dakika 30 sannan na budi baki na fara bata labarin kaman haka
XXXXXXXX
XXXXXXXXX
XXXXXXXXXX
kwance nake acikin shagona dake bayan gari aduk lokacin da'ake ruwa hankalina baya kwanciya har ruwan yadauke. Saboda dakin ginin kasane ko plasta babu abokaina dayawa sunsha bani shawara dana kauracewa wannan shagon amma ina nayi kunne shegu
ba komai bane yasa nake kaunar shagona illa a bayan gari yake kusa da kushewa hakan yasa nake aikata abinda raina yaga dama babu yansa ido
*********
can tsakiyar dare misalin karfe 1 zuwa 2 na dare ina kwance acikin shago na ina bacci me dadi
. Baccina ya katsene sakamakon karan kide kide da raye raye dana keji a gaba dani kadan
kida tashi yake me dan karan dadi wanda yasa harna fara rawa da kai kawai sainaji ansa wakan [wizkid sexy mama rmx] bansan lokacin dana tashi ba na nufi kofan dakina domin na bude naga komai akeyi a waje. hankali nabe kawomin tunanin komai ba ko wani abu zai'iya faruwa da rayuwa taba.
Bude kofan dakin nayi a hankali sannan na leka na hango inda nake jiyo kidan akwai dan nisa tsakanin sa da shagona.
Banyi tunanin haduwa da wani abuba dukda tsakiyar dare ne. kawai sainasa kai na fita na fara tafiya
nayi tafiya kaman na minti 3 kafin na kusa da inda nakejin kidan amma kuma daga wajen ina hango duk abinda akeyi awajen da alama party akeyi
Na hango kyawawan yan mata na gaban kwantance wanda inada yakinin cewa inda zan wuni inkwana ina gaya maku irin kyawunsu bazan fadi koda rabi ba.
Domin nasha kallon finafinan larabawa indiyawa american dss amma bantaba ganin kyakkyawan yan mata wayanda sukakai koda rabin suba a wajen kyau.
Abinda yakara ban mamaki damatukar al'ajabi shine yan matan rawan da sukeyi ya wuci hankalin me hankali domin cewa idan kida yayi kida yan matan hartashi sama sukeyi baza su dawo kasa ba sai sunyi kaman sakon 30 bugu da kari yan matan rawan da sukeyi suna juya gabban jikinsu kaman bana ...


This page:
Help/FAQ | Terms | Imprint
Home People Pictures Videos Sites Blogs Chat
Top
.