peperonity.net
Welcome, guest. You are not logged in.
Log in or join for free!
 
Stay logged in
Forgot login details?

Login
Stay logged in

For free!
Get started!

Mobile Blog


dadylasting.peperonity.net
13.05.2015 17:05 EDT
....DIREBAN HAJIYA....
Part 1
[adabin bariki]
.
.
Via taskar dadylasting me zamani .
.
Dadylasting.peperonity.net
.
.
Yanayin sararin samani dauke yake da tsananin hazo hakan yasa sassanyan garin yake dauke da tsananin sansanyan sanyi. Kusan kowa kagani agarin dauke yake da kayan sanyi dukdade da sassafene misalin karfe tara na safe {9:00am}
kana shigowa kan layin zakaji muryar wata kyakkyawar budurwa tana magana cikin sheshshekar kuka tana cewa.
Yanzu idan katafi kabarni yaya kakeso nasa kaina bayan kasan cewa da sonka nake kwana nake tashi. Kaine rayuwata sa'id nasan cewa idan katafi birni shikenan zaka manta dani saboda nasan cewa yan matan birni gwanaye ne wajen kwacen saurayi. Kuma kasan cewa kaina madubin rayuwata kai nake burin aure amma yanzu ka...............
Kyakkyawar budurwar takasa karasa abinda takeso ta fada sakamakon kuka dayaci karfinta
kyakkyawan saurayin dake tsaye agefenta wadda takirasa da said ya nisa kafin yace da ita cikin wata murya dayake nuna alamun tausayawa da jimami
FADILAT kinsan cewa inasonki bazan iya misalta tsananin tsagwaron yawan so da kaunar danake miki acikin zuciyata ba kullun sonki dada karuwa yake acikin zuciyata. Bawai tafiyata birni yana nufin cewa na rabu dake ba a'a saidai kawai nide burina inje insamo kudi amana aure in daukeki mutafi birni muyi zaman mu acan.
Yanzu de abinda zance miki shine ki kula da kanki kuma ki rikemin alkawari.
Fadila tace cikin muryarta dake nuni da tasha kuka tagaji. Tace karka damu said kaima kasan nafi kowa sonka.
Sa'id yacire wani kyakkyawan zaube a hannunsa yace ga wannan kisa a hannunki saboda ki tuna dani lokaci zuwa lokaci.
Tana karfa sa'id yajuya yayi mata sallama irinta masoya ya tafi yabarta cikin bakin cikin rabuwa da masoyi {rabuwa da masoyi sunan wani labarina ni dadylasting}
*** *** ***
sa'id yana komawa gida sallama yayi da iyayen sa da yan uwa da abokanan arziki.
Sannan ya nufi hanyar kano wajen wani abokin kawunsa alhaji musa.
Alhaji musa mutunne me tsananin arziki kuma dan siyasane sananne a birnin kano da kewaye.
Hakanne hasa danazo garin kano bansha wuya ba wajen neman gidan sa. Gidansa katon gidane kerarre inda zan wuni inkwana bazan gama wassafa maku yanayin kyawun gidan nasaba {kudai kuyi addu'a allah nuna maku kalan gidan koda a mafarki ne}
ina zuwa dayake alhaji musa ya fadawa me gadin gidan cewa zanzo. Ina zuwa bansha wuya ba wajen bayanin kaina. Kai tsaye me gadi ya wuce dani zuwa falon gidan wanda girman falon yakai girman gidan talakawa guda uku.
Tun kafin ni sa'id nakarasa cikin falon gidan bakaramin kauyanci nayi ba.
Ina shiga falon dani da baba me gadi kawai sai baba me gadi ya juya.
Ina karasawa cikin tsakiyan falon saina zauna akan kapet din falon nagaidar da alhaji musa bangama rufe bakina ba. Naji anyi sallama da wata siririyar murya me dadin ji da sauraro cikin sauri na daga kaina domin naga mahallakin dayayi maganar wata kyakkyawar mace nagani wadda kallo daya nayi mata naji gabana yafadi bakomai bane ya fadarmin da gaba illah kayan dake jikinta Sanye take da matsatstsun riga da wando masu tambarin kamfanin destiny,..yafe da wani dan guntun gyale iya kirji wanda be rufe asirin nonuwanta dake barazanar yage rigar ba saboda tudun su da girmansu...tabbas Allah yayi hallitta ta ko ina ta hadu musamman ta bangaren kayan alatu,.
a fakaice na kai ga kallo ga mazaunanta wani mahaukacin tudu da naga sunyi kaman an hura balam balan yasa naji yawuna ya tsinke tare da jin wani abu na tasowa daga kasan zuciyata
takaraso cikin harabar falon da wata irin tafiya mejan hankalin mazaje. Dakar na'iya saita tunanina kafin na tsugunar da kaina kasa.
Alhaji musa yace sa'id inaso kazauna damu amana kuma ka dauka tamkar mune iyayen ka. Aikin da zaka dinga yi mana agida shine zakana kai matata wajen aiki. Tana aikine a asibitin aminu kano teaching hospital saikuma zakana zuwa aike da bawa fulawowi ruwa. Ya juya ya kalli wannan kyakkyawar macen data shigo yace matata ta kaina ga direban nasamo maki sunansa sa'id tace yauwa nagode darlin
nikuma sa'id nace ina wuni hajiya kafin ta amsamin gaisuwata saida tafin wani farrr da ido wanda ni narasa gane ko namenene???
...


This page:
Help/FAQ | Terms | Imprint
Home People Pictures Videos Sites Blogs Chat
Top
.