peperonity.net
Welcome, guest. You are not logged in.
Log in or join for free!
 
Stay logged in
Forgot login details?

Login
Stay logged in

For free!
Get started!

Mobile Blog


dadylasting.peperonity.net

BASAJA 2016

17.01.2017 15:59 EST
is a true life story writing by jiddah haulat guru edited and collection by admin dadylasting via T.S SABUWAR BASAJA 2016
(Marubuta a hannun mata)
.
Matashin marubucin bai san cewa ranar asabat ce kaddara za ta fara kuka a kan rayuwarsa ba, kwarai kuka.
Da safe har zuwa karfe goma sha daya bai tashi a barci ba sai a lokacin da ya ji wayarsa ta fara 6urari, ya lalubota da sauri ya amsa tare da magagi, jin cewa
"Kai ne marubucin Madubi Sha Kallo? Aisha ce daga Abuja."
Babban dalili ne da ya sa shi wartsakewa. Tun bayan fitar da littafinsa, ya amsa wayoyi da yawa amma kuma wannan ya kalleta a ta daban, musamman ma da yaji muryar matar, irin ta manyan mata ce, matar ma kuma daga Abuja.
"Eh nine."
Ya amsa mata
"Na karanta littafinka ya min dadi."
Ta mayar masa, kamar yadda yake a al'adarsa sai yace
"Gyara fa ko shawara."
"A matsayinka na sabon marubuci dai ka yi kokari sosai, ban ga gyara ba ko shawara."
Haka dai abubuwa suka ci gaba da tafiya tana ta kiransa, shi kuma yana mata kallon babbar mace har zuwa ranar 11-02-2013 in da ta kutso rayuwarsa a dandalin whatsApp a matsayin budurwa 'yar shekara 22 Kacal da wani mayen hotonta mai fizgar hankali matuka!
.
Farko
"Yaushe littafinka zai fita nan gaba?"
Tambayar da ta fara masa kenan , shi kuma ya tura mata bangon littafinsa mai fita na gaba.
Daga nan hira ta tsinke, ta ci gaba da cewa
"Photon Dpnka yayi kyau , na nunawa 'ya'yan Auntyna har wani a cikinsu yake cewa 'wow I like this guy.'
Shi kuma yayi murmushi ya ci gaba da kallon fuskarta mai daukar hankali kafin ya mayar mata cewa
" Na ki ya fi daukar hankali."
Ta yi murmushi da godiya sa'an nan tace
" 'Yam matanka nawa?"
Ya mayar mata cewa
"Suna da yawa, amma wacce nake so ba ko daya."
Kamar haka take jira ya fada ta fara bashi labarin da bai bukata ba
"Ni kuma akwai masu sona da yawa, a ciki har da ma'aikacin rediyon V.O.A Nasiru El-Hikaya da dan gidan Chief Judge na Federal High Court inda Yayana yake Registerar , sa'an nan lokacin da na kammala sakandire akwai wani dan Yayan Babana da ya makale min da soyayya , har an sa ranar aure. A hanyarsa ta zuwa Gombe, ya yi accident ya mutu."
A wannan gabar datar marubucin ta kare, bai mata reply ba.
Bayan awa hudu ta kira shi da tuhumar ta ji shi shiru, shi kuma ya sanar mata datarsa ta kare.
Daga nan sako ya fado masa, ya duba ya ga kati ne. Kati makudai.
Ya mayar da su kudi, ya sayi data ya fara tambayarta dalilin da ya sa ta yin haka , a wannan lokacin ta fara shirga masa karya
"Wani saurayina ne da bana so ya turo min, ni kuma na turo maka."
.
Daga nan a duk lokacin da ta ji shi shiru sai ta tura masa kati da tsammanin datarsa ce ta kare, a farko ya nuna mata kuskuren hakan , amma ba ta bari ba.
Ta fara nuna masa alamun so shi kuma ya nuna bai gane ba.
Ya tambaye ta
"Ko kina facebook?"
Ita kuma ta mayar masa cewa
"A'a ko WhatsApp ma sai da na tambayi matar Yayana sa'an nan nake."
Ta fada masa , shi kuma barci ya dauke shi. Da sassafe yana tashi ya ga kiranta kusan 4 da bai daga ba, ta kira shi a tsakar dare da kuma da asubah.
Da ya gama abubuwan da zai yi, ya hau WhatsApp ,sakonta ya fara shigowa wayarsa
"Na shiga damuwa da na ji ka shiru?"
"Dalili?"
"Hmm nima ban sani ba."
"Mai yasa ba ki sani ba?"
"Wannan ma ban sani ba."
"Ke komai ba ki sani ba?
" Amsar kenan?"
Ya ja tsaki ya fita a bangonta ya Shiga duba sauran sakukkuna, da ya kammala ya ga sabbin sakonta biyu da bai duba ba
"Hmm ka share ni ko?" Da kuma "Ka cika Jan aji."
Shi kuma yace
"Ba Jan aji ba ne, tsarina ne haka."
Ta turo masa murmushi
"Dama wani labari zan baka."
"Na me?"
"Na saurayin da nake so."
"Waye?"
"Wani ne , dan kwalisa."
"Ta ya zan San shi."
"Marubuci NE fa."
"Akwai Marubuta da yawa, Dini Dan MASU Gari, Jamil Nafseen, Sani Ata, Ayuba Danzaki da sauransu."
"Duk ba ka canka ba, ni marubucin MADUBI SHA KALLO nake so."
Ya yi murmushi da tunanin dama ya san abun da zai faru kenan
Na tambayeta. "Me yasa kike son Marubucin Madubi Sha kallo?" Ta amsa da "Haka kawai na ji zuciyata na sonsa" Haka dai na amsa ma ta da nima ina sonta, ko ba dan komai sai yanda na ga a matsayinta na kyakkyawar budurwa mai aji ta firta kalmar so a gareni, tukwicinta gareni shi ne amsar bukatarta hannu biyu ko da kuwa a iya fatar baki ne. Tun daga wannan ranar muka fara soyayya ni da Aishan Abuja haifaffiyar Gombe (kamar yanda ta sanar min). Ta fito min a fuskar kamala da kamun kai matuka. Inda cikin hirarrakin da mu ke ne ta ke fada min Yayanta na da zafi, ta yanda baya barinta fita ko ina, daga makaranta sai gida. Hatta da irin kawayen nan da 'yan mata ke yi na debe kewa Aisha ba ta da su. Su kadai su ke rayuwarsu cikin gida, sabida tsaro da ta-ka-tsan-tsan irin na Yayanta. Ita kuma a matsayinta na mai tarviyya da bin umarni yasa ta yin biyayya gami da kare duk wata doka ta sa. Soyayyarsu ta fara nisan da har idan bai ga Aisha a online ba baya samum nutsuwa da kwanciyar hankali. Hatta da chart din kansa fita ya ke daga zuciyarsa kwata-kwata, dan baya gane abin da ya ke karantawa. Duk a dalilin rashin Indonsa a online. Yau din ma hakan ce ta kasance. Dan haka tun bayan sallarsa ta asuba ko addua bai tsaya yi ba ya dauko wayarsa ya kunna data. Jerangwayen notifications ne ke barazanar fasa masa waya da karararrakin shigiwarsu. Cikin sakwanni kuwa har da na Amininsa Deeni DAN MASU GARI, da na Bamai Kwaske. Duk bai bi ta kansu ba. Fatansa da burinsa kawai ya ga shigowar sakon Aisha INDOnsa. Wacce ke kokarin sace zuciyarsa da budurwarsa Talatu Kwaila ta gama shukar soyayyarta da tai tsiro ta na kan shirin nomewa. Amma cikin abinda bai wuce sati biyu ba ga bakuwa ta na neman mata mamaya a cikinta.. Idonsa kan last seen dinta. Wanda ya nuna masa rabonta da online tun 12:59 na daren shekaranjiya da su kai sallama. Hankalinsa ya kara tashi, anya kuwa Aisha lafiya? Dan tun haduwarsu ba su taba haura awa daya ba, ba tare da sun yu charting ba. Su na sauka kuma za ta kira shi a waya su bata lokaci suna soyayya. Har a zuciyarsa ya na mamakin irin kudin da ta ke konawa gurin making call kawai. Dan shi ya saba, da ga flashing sai please call me. Idan ta baci kiran ya Zama dole shi ne zai kira ka ya ma magana ba tare da sallama ko gaisuwa ba, ya isar da sakonsa, wanda hakan baya wuce abin da ya kai sakwan 20 zuwa 30 shi ma sai idan ta baci... Dan shi ya saba sai dai a kirasa ba dai ya kira ba. Albashinsa da dan kudinsa sun fi karewa ne a kan sumar kansa da sutturar jikinsa. Dan hatta da cikinsa ma bai yarda ya ba shi abinxin da Zai cinye sama da naira dari ba. Duk garinsu ya fi kowa gayu, shi ya sa ya ke rikita yan matan garin har ma da zawarawan garin. Ga shi dan gayu ajin farko ga shi marubuci. Ba tare da ransa ya so ba, dan kawai zuciyarsa ta azalzaleshi ne ya sa ya dauki wayarsa ya fara neman lambar INDOnsa dan ya ji ko lafiya. Amma a ransa ya na jin zafin asarar kudin kiran da zai yi na yau. Shi ya saba sai dai a kirasa ba dai ya kira ba. (Kun ji irin wayon marubuta. LOL). Like · 5 · Reply · Report · Yesterday at 3:33pm Yusuf U Sanka Slm Like · 1 · Reply · Report · Yesterday at 3:36pm Haj Aisha Farhan Tnx # Jiddah Like · 1 · Reply · Report · Yesterday at 3:38pm Mustapha Abbas Auyon? Like · 2 · Reply · Report · Yesterday at 3:38pm Mas'uud Musa Bakoree Tanx Like · Reply · Report · Yesterday at 3:40pm Abubakar Abdul-hadi tnx Like · 1 · Reply · Report · Yesterday at 3:49pm Jiddah Haulat Nguru 4. Cikin sa'a kuwa wayar ta shiga. Zuciyata cike da fargabar idan ta dauka me zance ma ta. Kasancewar yau ce rana ta farko da na taba nemanta ta waya. Ta na ringing har ta katse ba'a daga ba. Shiru nai da waya a kunnena, duk da kuwa service ya nuna min tsinkewar wayar ta hanyar karar da ta yi bayan ringing na karshe. Ban gaza ba a karo na biyu na kara kiran wayar, shi ma har ta tsinke ba'a dauka. Nan zuciyata ta ci gaba da karantomin sakokin da ta ke sakawa kala-kala. Ban kai ga zabar dayan cikinsa bw wayartawa ta hau kuwwa alamun kira ya shigo. "Aisha ce." Na fada a fili cikin murna tamkar wani na ji na. Ban bata lokaci ba gurin amsa kiran. "Sorry Abubakar ka ji ni shiru ko?" Ta fada bayan na amsa kiran, ban kuma kai ga ce wa komai ba. "Shi ne na neme ki na ji ko lafiya" Na fada cike da kulawa. Can na ji kamar saukar nishi sama-sama ta wayar. Daman tun farkon maganarta na ji ta ba yanda mukq saba ba. "Ni kam lafiyar ce ta min karanci." Ta ban amsa. Yayin da muryarta ke nunin gaskiyar abinda ta fada. Nan take
Like · Reply · Edit · Dec 2, 2016
Hadejia road kano
SABUWAR BASAJA 2016 (Marubuta a hannun mata 5. Cike da kulawa cikin muryar tausayi tamkar tana kallona na ce, "Subhanallahi ! Me ya same k Aysha" Sai da ta saukar da naunauyar ajiyar zuciya kafin cikin sanyin murya irin ta marasa lafiya ta ke ce min. "Wallahi Abubakar ba ni da lafiya ne. Tun shekaranjiya da muka rabu nake fama har yanzu." "Me ya same ki Aysha, wanne irin ciwo ne haka, ba ku je asibiti ba?" Na jeho mata wadannan kidimammun tambayoyin da ba za su amsu a tare ba, sai daya bayan daya. "Kar ka damu. Yanzu da sauki ba kamar jiya ba ma. Yanzu haka ina asibiti tun daren shekaranjiyan akai admitting dinmu. Ciwon ciki ne ya ke damuna..." Da kyar ta karashe wannan dan dogon bayanin. Da alamu har yanzu ta na jin jiki. "Wanne irin ciwon ciki ne mai tsanani haka?" Na tambaya cike da kulawa gami da tausayinta cikin raina. "Uhmm! " kawai ta ce tai shiru. "Umhuum ina jin ki." Na fada cike da son jin karin bayani. "Uhm!... Uhm!!.. Daman ba wani abu bane.... Kawai idan karshen wata ya zo haka na ke yi. So Kullum muka zo asibitin ba sa bamu komai sai magani. Anyi scanning da duk gwaje-gwaje an ce wai ba a ga komai ba. Amma dai Yayana ya gaji ya ce matukar This time ba su gano komai ba za mu fita waje a duba. Dan abun yayi yawa." Nan ta ke na gano matsalarta ta. Cike da jin dadin alkunya da kamun kai irin na ta, na yanda ta kasa bayyana min irin ciwon na ta kai tsaye na kara jin sonta a zuciyata ya mamayu. Ina son mace mai kunya!. "Gaskiya ...


This page:
Help/FAQ | Terms | Imprint
Home People Pictures Videos Sites Blogs Chat
Top
.